Gwamnatin Tarayya tace tana duba yiwuwar tsayar da tafiye-tafiye tsakanin jihoshi da gari zuwa gari, in banda wanda ya zama tilas, daga cikin matakan dakile yaduwar cutar coronavirus.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da haka a Abuja yayin taron manema labarai domin bayar da bahasi akan matakan da gwamnati take dauka wajen dakile cutar.
Ministan ya jaddada cewa lokaci yana kurewa kuma akwai bukatar manyan matakan gaggawa wajen magance annobar.
Lai Mohammed ya tabbatar da cewa matakan da aka dauka kawo yanzu wajen dakile annobar na aiki, duk da kasancewar akwai sauran rina a kaba.
Lai Mohammed ya yabawa shawarar kamfanonin jiragen sama 5 wajen dakatar da jigilar jiragensu, kamfanonin sune Air Peace da Aero da Azman da Dana da kuma Arik Air.