Gwamnatin Jihar Binuwai tace ta kama makiyaya 400 bisa laifin karya dokar hana kiwo a sarari a jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma kwace shanu sama da 600, mallakar makiyayan.
Gwamnan Jihar, Samuel Ortom, wanda ya bayyana haka a Makurdi, ya umarci dakarun kula da dabbobi da su kama dukkan saniyar da suka gani tana kiwo a sarari a ko’ina cikin fadin jihar.
Samuel Ortom ya bayar da umarnin yayin da yake duba shanun da aka kama a sashen killace dabbobi na ma’aikatar aikin gona ta jihar.
Yace tursasa aiki da dokar hana kiwon a sarari zata cigaba da aiki domin bayar da dama domin wadanda suke da niyyar sana’ar kiwo su kiyaye tanadinta.
Da yake bayyana kwararowar makiyaya zuwa jihar a matsayin barazana ga rayuka, gwamnan yace gwamnatinsa baza ta lamunci hakan ba.