El-Rufa’i Ya Nada Muhammad Sanusi II A Matsayin Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna

73

Awanni 10 kacal bayan bashi mukamin mataimakin shugaban hukumar bunkasa zuba jari na jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya sake ambatar sunan Sarkin Kano Murabus, Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban jami’ar jihar Kaduna.

A wata sanarwar data fito daga gidan Sir Kashim Ibrahim na gwamnatin jihar Kaduna, wacce ta sanar da sabon nadin, tace Sanusi ya gaji shugaban jami’ar na farko, Mai Martaba Mallam Tagwai Sambo, Sarkin Moro’a, wanda aka nada a shekarar 2005.

Sanarwar wacce mai bawa gwamnan jihar shawara na musamman akan kafafen yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, tace Muhammadu Sanusi II ya nuna jajircewa sosai akan harkokin ilimi.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Nasir El-Rufa’I ya aika da sakon dumbin godiyar gwamnati zuwa ga Mai Martaba Mallam Tagwai Sambo, bisa aikin da yayiwa Jami’ar Jihar Kaduna, dama jihar baki daya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 14 =