Buhari Ya Amince Da Sakin Kudi Naira Biliyan 10 Ga Jihar Lagos Saboda Coronavirus

51

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da wasu ka’idoji dangane da annobar cutar coronavirus wacce ke yaduwa kamar wutar daji da kuma kokarin gwamnatinsa wajen magance ta, ciki harda amincewa da sakin kudi naira biliyan 10 ga gwamnatin jihar Lagos, bisa bukata.

Ya kuma ce an amince da sakin kudi naira biliyan 5 ga cibiyar magance yaduwar cututtuka domin samar da kayan aikin da zasu taimaka wajen daukin gaggawa.

Martanin shugaban kasar yazo ne daidai lokacin da ake tsaka da yi masa adawa cewa yana nuna halin ko’in kula yayin da cutar ke fatattakar kasarnan.

Kakakinsa, Mallam Garba Shehu, cikin wata sanarawa, ya jiyo Buhari yana shawartar dukkan ‘yan Najeriya da su kiyaye wajen bin ka’idojin kiwon lafiya wanda ma’aikatar lafiya ta tarayya ta bayar, tare da gwamnatocin jihoshi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 14 =