An Kusa Hana Fita Daga Gida a Lagos Saboda Coronavirus

34

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu yace nan bada jimawa ba za a hana fita kwata-kwata a jihar muddin aka cigaba da kamuwa da coronavirus.

Sanwo-Olu ya fadi haka lokacin da yake bayar da bahasi akan halin da ake ciki dangane da annobar a jihar, a gidan gwamnatin Lagos dake Marina.

Sai dai, tunda farko, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, a wani taron manema labarai, yace za a iya samun mutane dubu 39 da suka kamu da cutar ta covid-19 a jihar, lamari mafi muni da zai iya faruwa.

Abayomi daga nan sai ya bukaci mazauna jihar da su kiyaye wajen bayar da tazara ga juna, domin dakile yaduwar cutar.

Kwamishinan ya kara da cewa jihar na neman mutane dubu 3 wadanda watakila sunyi mu’amala da wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 5 =