Za A Iya Fuskantar Karancin Mai Kasancewar Direbobin Tankokin Mai Sun Tafi Yajin Aiki

74

Kungiyar direbobin tankar mai tare da kungiyar NARTO, sun shiga yajin aiki na sai baba ta gani, bisa zargin cin zarafin ‘ya’yan kungiyar da jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kwastan ke yi.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar NARTO ta kasa, Yusuf Othman, ya fitar, yace sun shiga yajin aikin sanadiyyar kame wasu tankokin mai ba bisa ka’ida ba, a jihoshin Kebbi da Kano da Katsina da sauran jihoshin Arewa, da jami’an kwastan suka yi.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar direbobin tankar mai, Sa’idu Al’amura, yace kungiyar taga dacewar tafiya yajin aikin, domin su bayyana damuwarsu bisa zargin cin zarafi tare da kame ‘ya’yan kungiyarsu, a kan hanyarsu ta zuwa gidajen mai, har a cikin kwaryar birnin Kano.

Da aka nemi jin ta bakinsa, jami’in hulda da jama’a na hukumar hana fasa kwauri, shiyyar Kano da Jigawa, Danbaba Isah, ya tabbatar da kamen tankokin mai 5 bisa zargin karkatar da mai daga Kano zuwa garin Faggo a yankin karamar hukumar Sandamu, ta jihar Katsina.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × three =