
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta jajirce sosai wajen ganin bayan ta’addanci da hare-hare da dukkan ayyukan tada zaune tsaye a Najeriya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka yayin da yake bukatar ‘yan Najeriya su mara baya tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro, wadanda suke a shirye wajen kare tare da tsare hadin kan kasarnan.
Da yake jawabi yayin zaman tattaunawa tare da mambobin kwamitin kungiyar ‘yan Najeriya a kasar Habasha wanda aka gudanar a birnin Addis Ababa, shugaban kasar ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya a gida da waje cewa tsaron lafiyarsu zai cigaba da zama babban abinda gwamnatinsa ta saka a gaba, tare da yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawo karuwar arziki ga ‘yan Najeriya.