Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Injiniya Ahmed Kadi Amshi da wasu mutane 11 a matsayin shugaba da mambobin hukumar kula da majalisun kasa.
An gudanar da bikin kaddamarwar a zauren fadar shugaban kasa dake Abuja.
Sabon shugaban hukumar kula da majalisar, Ahmed Kadi Amshi, yana wakiltar jihar Yobe ne, a Arewa maso Gabas.
Sauran mambobin hukumar sune Babagana Modu, Jihar Borno, Arewa maso Gabas; da Abubakar Tutare, Jihae Taraba, Arewa maso Gabas; da Hakeem Akamo, Jihar Lagos, Kudu Maso Yamma; da Tunrayo Akintomide, Jihar Ondo, Kudu Maso Yamma.
Sauran sune Bassey Etuk, Jihar Akwa-Ibom, Kudu Maso Kudu; da Bailyaminu Yusuf Shinkafi, Jihar Zamfara, Arewa Maso Yamma; da Sani Saidu Kazaure, Jihar Jigawa, Arewa Maso Yamma; da Julius Ucha, Jihar Ebonyi, Kudu Maso Gabas; da Auwalu Aliyu Ohindase, Jihar Kogi, Arewa ta Tsakiya, da Muazu Is’haq, Jihar Nasarawa, Arewa ta Tsakiya da kuma Atanomeyorwi Francis, Jihar Delta, Kudu Maso Kudu.