Ofishin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa a Jigawa ya Tara Harajin Naira Biliyan 6 da Miliyan 400 a 2019

32

Ofishin hukumar tara kudaden shiga ta kasa a jihar Jigawa ya tara harajin naira biliyan 6 da miliyan 400 a shekarar 2019 da ta gabata.

Jami’in hukumar a jihar nan, Alhaji Sa’idu Ibrahim Gabari ya bayyana haka a taron karrama wadanda suka baiwa hukumar gudummawa da aka gudanar a babban dakin taro na sabuwar sakateriya.

Ya ce hukumar zata kara kaimi domin rubanya kudaden harajin da ta tara a wannan shekarar, kuma sun shirya taron ne domin karrama wadanda suka yi fice wajen ci gaban hukumar.

A nasa jawabin gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi, Alhaji Babangida Umar Gantsa ya ce gwamnati zata ci gaba da baiwa hukumar hadin kai da goyan baya domin kara samun kudaden shiga a shekaru masu zuwa.

Ya bayyana gamsuwa kan yadda hukumar ta karrama gwamna Muhammad Badaru Abubakar da kuma sauran mutane, wanda a cewarsa hakan zai bada kwarin gwiwa ga al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − 4 =