Masu Zanga-Zanga Sun Kai Farmaki Zuwa Sakatariyar Jam’iyyar PDP a Bayelsa, Inda Suka Cinnawa Wani Sashen Ginin Wuta

31

A wani cigaban kuma, masu zanga-zanga sun kai farmaki zuwa sakatariyar jam’iyyar PDP a Yenagoa na jihar Bayelsa, inda suka cinnawa wani sashen ginin wuta.

An rawaito cewa mutanen wadanda aka batawa rai, suna zanga-zanga kin amincewa da hukuncin kotun koli, suna jifa da dunkulen wuta zuwa sansanin sakatariyar ta PDP.

Sai dai, an samu labarin cewa wutar ta shafi injin bayar da wutar lantarki da dakin masu gadi.

Masu zanga-zangar sun kuma cigaba da bayyana bakin cikinsu inda suka farwa ginin kotunan jihar, bayan sun yi kokarin kona wani sashe na ginin.

Amma an rawaito cewa daukin gaggawa na hukumar kashe gobara ta jihar ya kawo karshen wutar da take ci a sakatariyar jam’iyyar ta PDP da kuma ginin kotunan.

Masu zanga-zangar wadanda suka mamaye manyan tituna, an kuma bayar da rahoton cewa sun kai farmaki zuwa ginin gidan rediyon Bayelsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 3 =