Kotun Koli ta Soke Zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

41

Kotun Koli ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa mai jiran gado, David Lyon tare da mataimakinsa.

Kotun kolin karkashin jagorancin mai sharia Mary Odili, ta bayar da umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta kwace takardar shaidar lashe zabe da ta bawa ‘yan takarar na jam’iyyar APC wadanda a baya aka ayyana su a matsayin wadanda suka lashe zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwambar bara.

Kotun mai alkalai 5 ta kuma umarci hukumar zaben ta INEC da ta bayar da sabbbin takardun lashe zabe ga ‘yan takarar jam’iyya ta 2 mafi yawan kuri’un da aka kada.

Mai shari’a Ejembi Ekwo ta sanar da hukuncin bayan soke cancantar dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a matsayin dan takara a zaben.

Kamar yadda yake a sabon hukuncin, dan takarar jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u Dubu dari da arbain da uku da dari da sabain da biyu ya zama shine wanda ya lashe zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + fourteen =