Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, daga soke wasu jam’iyyun siyasa.
Mai shari’ah Anwuli Chikere, ta bayar da umarnin biyo bayan shigar da karar da wasu daga cikin jam’iyyun da abin ya shafa suka shigar.
Mai shari’ar, a hukuncin da ta yanke, tace hukumar zaben ta INEC ta gaza mayar da martani ga masu shigar da kara, wadanda ya zama tilas a kare musu hakkokinsu.
An bayar da rahoton yadda hukumar zaben ta INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, yace matakin yana daga cikin shirye-shiryen zabukan gama gari na shekarar 2023.
Shugaban hukumar yace soke jam’iyyun ya biyo bayan rashin taka rawar gani da suka yi a zabukan gama gari na shekarar 2019.