Kimanin ‘Yan Gudun Hijirar Kamaru Dubu 8 Ne Suka Yi Kaura Zuwa Najeriya Cikin Makonni Biyun Da Suka Gabata

43

Kimanin ‘yan gudun hijirar Kamaru dubu 8 ne suka yi kaura zuwa gabashi da kudancin Najeriya cikin makonni biyun da suka gabata, a cewar hukumar kula da gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, bayan tashe-tashen hankula ya karu tsakanin jami’an tsaro da mayakan ‘yan aware.

Karuwar ‘yan gudun hijirar, wanda yazo gabannin zaben gama gari na karshen makon da ya gabata, ya kawo yawan yan kasar Kamaru da suka yi kaura zuwa Najeriya kimanin dubu 60, a cewar hukumar ta majalisar dinkin duniya.

Rikici tsakanin sojin Kamaru da mayakan tsagen masu amfani da yaren Ingilishi masu neman a ware musu kasar Ambazonia, ya fara bayan gwamnati ta fatattaki masu zanga-zangar lumana, wanda ke korafin ana nuna musu wariya daga masu amfani da harshen faranshi mafiya rinjaye.

Rikicin ya tursasawa mutane rabin miliyan kauracewa gidajensu tare da gabatarwa shugaban kasar Paul Biya babban kalubale tun bayan darewarsa kan karagar mulki kimanin shekaru 40 da suke gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen + 20 =