Jam’iyyar PDP ta Bukaci Kotun Koli ta Bibiyi Hukunce-Hukuncenta

64

Jam’iyyar PDP ta bukaci kotun koli da ta bibiyi hukuncinta da ya tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shakerar 2019, tare da korar daukaka karar dan takararta na zaben shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Kakakin jam’iyyar ta PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, wanda ya sanar da haka yayin taron manema labarai a Abuja, ya kuma yi kira ga kotun kolin data bibiyi hukunce-hukuncenta na zaben gwamnanonin jihoshi 4, jihoshin sune Osun da Kaduna da Kano da hukuncin kotun kolin kan zaben gwamnan jihar Katsina.

Amma da yake mayar da martani kan matsayar jam’iyyar PDP, sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya shawarci jam’iyyar adawar ta PDP da ta koma gona ta fara noman shinkafa kasancewar bata da aikin yi tun bayan faduwa zaben gama gari na shekarar 2019.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + 7 =