Kungiyar Dattawan Arewa tace abin takaici ne kin amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sasanta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi.
Dattawan kungiyar sun ce kin amincewar shugaba Buhari na sasanta Ganduje da Sarki Sanusi, abin Allah wa dai ne.
Ana ta samun rikita-rikita tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi, biyo bayan kirkirar karin masarautu a jihar Kano.
Anyi amanna a wasu guraren cewa Gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masarautun domin rage karfin fada ajin Sarki Sanusi a jihar.
Duk da rikita-rikitar tsakanin manyan mutane Kanon guda 2, Shugaba Buhari yaki amincewa ya tsoma baki a lamarin, inda ya bayyana hujja da kangewar kundin tsarin mulki.
Sai dai, kakakin kungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya ce ikirarin shugaban kasar na rashin ikon tsoma baki a irin wannan rashin jituwar, sanadiyyar kangewar kundin tsarin mulki, bashi da tushe.