Bankin Duniya Ya Amince Da Kashe Kudi Naira Biliyan 799 da Miliyan 700 Domin Ayyuka a Najeriya

29

Bankin Duniya ya amince da gudanar da ayyuka guda 6, wadanda kudinsu ya kai kimanin Dalar Amurka Biliyan 2 da Miliyan 200, kwatankwacin Naira Biliyan 799 da Miliyan 700, domin aiwatarwa a Najeriya, a shekarar 2020.

Shugabannin Bankin sun zauna domin tattaunawa akan wata bukata daga gwamnatin tarayya.

A wata sanarwa da bankin ya fitar, yace ayyukan zasu taimakawa cigaban jama’a da na tattalin arziki, da zummar fitar da miliyoyin ‘yan najeriya daga kangin talauci.

A cewar sanarwar, abubuwan da bankin ya amince da su zasu taimaka wajen samar da kudaden ayyukan da zummar inganta rigakafi da kirkirar yanayin kasuwanci mai karfi domin bangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu, tare da fadada tattalin arziki na na na’ura mai kwakwalwa, domin samar da ayyukan yi.

Ayyukan suna kuma neman kara shigar da bangaren gwamnati da na ‘yan kasuwa wajen gudanar da mulki, tare da samar da kariya ga yanayin walwalar jama’a.

Daraktan bankin na kasarnan, Shubham Chaudhuri, yayi bayanin cewa za ayi ayyukan da nufin inganta samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − twelve =