Babbar Kotun Tarayya ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Olisah Metuh

37

Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai kan tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisah Metuh, tare da kamfaninsa mai suna Destra Investment Limited.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan ta same shi da laifin sama da fadi da kudi naira miliyan 400.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai shari’a Okon Abang, ya ce ya samu tsohon jami’in na PDP ne da laifin halatta kudin haramun.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsawo, Kanar Sambo Dasuki.

Alkalin yayi watsi da ikirarin lauyan wanda ake kara na cewa ba za a iya yankewa wanda yake karewa hukunci kan badakalar kudade ba, saboda Sambo Dasuki, wanda a halin yanzu yake fuskantar tuhuma, har yanzu ba a yanke masa hukunci akan laifukan cin amana da rashawa ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 10 =