Asusun TETFUND Ya Zargi Malaman Jami’a Da Karkatar Da Kudaden Bincike Wajen Gina Gidaje Da Sayen Motoci

30

Asusun manyan makarantu TETFUND ya zargi lakcarori a manyan makarantun gwamnati na fadin kasarnan da karkatar da kudaden bincike wajen gina gidaje, sayen motoci da facaka.

Wannan yazo kwanaki kadan bayan zargin aringizon kudaden albashi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta yiwa wasu makarantu da asibitoci, cikinsu har da jami’ar Ibadan, ya fito fili.

Da yake gabatar da sabon zargin a Birnin Dubai na Daular Larabawa, Daraktan Bincike da Cigaba da Asusun TETFUND, Salihu Bakari, yace yawanci ana wadaka da makuden kudaden da ake baiwa daidaikun lakcarori, wani lokacin a kungiyance, domin aikin bincike, da halartar taron gabatar da makalu da sauransu.

Salihu Bakari yayi jawabi a taron karawa juna sani wanda hukumar asusun ta shirya domin ma’aikatan sashen bincike da cigaba na wasu makarantun gwamnati, a wani bangare na kokarinta na garanbawul a ayyukan bincike a manyan makarantun gaba da sakandire na Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − eight =