Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, yace an samu bullar zazzabin Lassa a kimanin jihoshi 27 na kasarnan, a kididdigar baya-bayannan.
Osagie Ehanire ya fadi haka yayin tattaunawa da kwamishinonin lafiya na jihoshin kasarnan 36, a wani taro na wuni 2 wanda kungiyar gwamnonin Najeriya ta shirya a Abuja.
Ya kuma bayyana irin cigaban da gwamnatin tarayya ke samu wajen samar da rigakafin cutar, tare da hadin gwiwar wani kamfanin bincike na kasar Jamus.
Gwamanoni 36 karkashin kungiyar gwamnonin, sun fada a watan Janairun da ya gabata cewa gwamnatocin jihoshi na aiki kafada da kafada da sauran hukumomin lafiya domin dakile barkewar zazzabin.
Akalla mutane 16 ne kawo yanzu suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin a jihar Ondo, yayinda aka samu cutar a jikin mutane 84 tun farkon wannan shekarar.
A jihar Kano, zazzabin ya kashe mutane 3, wadanda suka hada da mace mai dauke da juna biyu tare da likitoci 2, bayan an duba su a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.