‘Yansanda Sun Ceto Wasu ‘Yanmata 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

55

Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina sun ceto wasu yanmata 6 da akayi garkuwa da su a yankin karamar hukumar Batsari ta jihar.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, SP Gambo Isah, wacce aka fitar a Katsina, ‘yansandan sunce an sace yanmatan yayinda suke aiki a gona a kauyen Mata-Mulki a karamar hukumar ta Batsari.

Gambo Isah yace yansanda sun samu kiran daukin gaggawa da misalin karfe 12 da rabi na rana cewa wasu maharan da basu tuba ba dauke da bindiga samfurin AK47 sun sace wasu ‘yanmatan dake aiki a wata gona a kauyen Mata-Mulki.

Kakakin na ‘yansanda ya kara da cewa jami’an operation Puff Adder karkashin jagorancin DPO na Batsari sun gaggauta zuwa yankin inda suka ceto yanmatan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × five =