Yansanda a Zamfara Sun Cafke Mutane 3 Dauke Da Bindigogi a Gusau

293

Tawagar ‘yansanda ta musamman ta operation Puff Adder ta cafke mutane 3 dauke da bindigogi a boye cikin buhunhuna a kusa da yankin Lalan a Birnin Gusau na jihar Zamfara.

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan, SP Mohammed Shehu, yace an kame wadanda ake zargin biyo bayan samun bayanai.

Yace wadanda ake zargin su 3 ana biye da su tun farkon tasowarsu daga Karamar hukumar Maradun ta jihar, har zuwa lokacin da aka kame su.

Jami’in yace wadanda ake zargin suna da shekaru 60 da 50 da kuma 35 a duniya, kuma an kama su dauke da bindigogin da aka kera a gida guda 4 da adduna da kuma gatari.

Mohammed Shehu ya bayyana cewa wadanda ake zargin sunyi ikirarin cewa mafarauta ne su, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Kogi domin farauta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + eighteen =