Wasu Mutane Da Ake Zargin Barayi Ne Sun Kashe Wani Dan Achaba A Jihar Jigawa

35

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe wani matashi dan shekara 27, mai suna Nura Abdullahi dan kauyen Hantsaki cikin yankin karamar hukumar Miga a nan jihar Jigawa.

Kakakin rundunar yansanda na jihar Jigawa, DSP Abdu Jinjiri Dutse, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Yayi bayanin cewa lamarin ya auku ne a ranar 6 ga watan Janairu da misalign karfe 3 na yammaci, bayan an gano wata gawa a cikin daji da rauni a fuskarta.

Ance mamacin dan achaba ne a kasuwar Gujungu.

Abdu Jinjiri yace ana zaton barayin babura suka hau babur din marigayin zuwa wani waje, inda suka far masa tare da kashe shi kuma suka arce da babur dinsa.

Yace an bayar da gawar ga ‘yan’uwan mamacin domin binnewa bisa koyarwar addinin Islama.

Kakakin yansandan yace ana gudanar da bincike domin cafke barayin wadanda suka gudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 3 =