Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa Yayi Kira ga Shugaba Buhari Yayi Murabus

33
Muhammadu Buhari

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga karagar mulki sanadiyyar karuwar rashin tsaro a kasarnan.

Sanatan yayi kiran a yau Laraba yayinda majalisar dattawa ke tattaunawa akan kudirin kalubalen tsaro na kasa tare da bukatar yin garanbawul a tsarin tsaron kasarnan.

Mista Abaribe wanda shine na farko da ya bayar da gudunmawa akan kudirin, ya dora laifi akan shugaban kasa bisa kasawarsa wajen dakile kalubalen tsaro a kasarnan.

Sanatan ya bayyana takaicin dalilan da suka sanya shugaban kasar yayi ikirarin cewa yana mamaki dangane da karuwar rashin tsaro a kasarnan.

Ya kuma kalubalanci kakakin shugaban kasa bisa kiran kungiyar kiristoci ta kasa a matsayin jam’iyyar siyasa saboda tayi Allah wadai da kashe-kashen kungiyar Boko Haram.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + two =