Shugaba Buhari Yace Rayuwa Mai Kunci Na Jiran Mahara Wadanda Ayyukan Ta’addancinsu Ya Jawo Damuwa Ga ‘Yan Najeriya

51

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace rayuwa mai kunci na jiran mahara da barayi wadanda ayyukan ta’addancinsu ya jawo damuwa ga ‘yan Najeriya, da raba mutane dayawa daga guraren cin abincinsu, tare da habaka tabarbarewar tsaro a kasarnan.

Shugaban kasar ya bayyana haka yayinda ya karbi tawagar manya da amintattun ‘yan asalin jihar Neja, karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Buhari ya dage kan cewa ayyukan maharan sun tursasawa mutane da dama barin gidaje da gonakinsu.

Yace hare-haren maharan ya kuma shafi yawan amfanin gonar da ake girbewa a wasu sassan kasarnan, dukda samun damuna mai albarka, kasancewar an fatattaki dayawa daga cikin manoma, yayinda sauran ke gujewa zuwa gonaki saboda rashin tsaro.

Shugaban kasar yace matakin talauci a kasarnan zai ragu sosai ta hanyar fadada aikin gona, akan dogaro kacokan da albarkatun mai, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su koma gona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − 5 =