Majalisun Kasa Sunyi Kiran a Samu Sauyin Shugabannin Tsaro na Kasa

20

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawa sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige shugabannin tsaron kasarnan tare da nada wasu sababbi.

‘Yan majalisar sun yi kiranne yayinda majalisar ke tattaunawa akan kudirin kalubalen tsaron kasa da kuma bukatar yin garanbawul a tsarin tsaron kasarnan.

‘Yan majalisar sun ware ranar yau Laraba gabadayanta domin tattaunawa akan matsalar. Hakan a cewarsu yazo ne sanadiyyar karuwar tabarbarewar tsaro a kasarnan.

A wani cigaban kuma, ‘yan majalisar wakilai na tarrayya sun bukaci shugabannin tsaron kasarnan da su ajiye aiki bisa karuwar tabarbarewar tsaro.

‘Yan majalisar yayin tofa albarkacin bakinsu daban-daban akan muhawarar da ake yi dangane da rashin tsaro a fadin Najeriya, sun bayyana damuwa akan rashin tabbas wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kasarnan.

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar ta wakilai, Jimi Benson, ya nuna takaicin yadda aka dauki lokaci mai tsawo har yanzu sojojin Najeriya da ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro sun kasa kawo karshen ‘yan ta’adda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 3 =