Sama da mutane 2,000 ne suka kamu da sabuwar kwayar cutar Coronavirus, mafiya yawansa a kasar China, inda mutane 56 suka mutu sanadiyyar cutar, kuma kasar Amurka tace zata kwashe wasu daga cikin ‘yan kasarta daga birnin wanda shine inda cutar ta barke.
Shugaban Kasar China, Zi Jinping ya fada yayin zaman tattaunawa jiya Asabar cewa kasar ta China na fuskantar babban kalubale, bayan hukumomin lafiya a fadin duniya na kokarin dakile yaduwar cutar.
Kwayar cutar wacce aka yi amannar cewa ta samo asali a shekarar bara a wata kasuwar abincin dabbobin ruwa a birnin tsakiyar China na Wuhan, inda aka sayar da namun daji ta haramtacciyar hanya, ta yadu zuwa biranen China wadanda suka hada da Beijing da Shangai da kuma kasar Amurka da Thailand da Koriya ta Kudu, da Japan da Australia da Fransa da kuma Canada.
A yau Lahadi China ta sanar da haramta sayar da namun daji a guraren cin abinci da kasuwanni a fadin kasar. Ana dora alhakin yaduwar cutar daga namun daji inda a jikinsu kwayar cutar ke hayayyafa su girma daga nan su koma jikin mutane.
A yau lahadi, kasar China ta tabbatar da mutane 1,975 sun kamu da sabuwar kwayar cutar ta Coronavirus zuwa jiya Asabar, yayinda mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar suka kai 56.