Isara’ila Ta Shirya Sojojinta Akan Shirin Ko Ta Kwana Bayan Kisan Da Amurka Ta Yiwa Qassem Soleimani

87

Isara’ila ta shirya sojojinta akan shirin ko ta kwana kuma Fira-Ministan kasar, Benyamin Netanyahu ya katse ziyararsa zuwa kasar waje, bayan kisan da Amurka ta yiwa kwamandan sojin Iran, Qassem Soleimani, lamarin da ya jawo alkawarukan daukan fansa daga Iran.

Isra’ila wacce ita ce kawar Amurka ta kut da kut a gabas ta tsakiya kuma babbar abokiyar hamayyar Iran, bata mayar da martani ba dangane da mutuwar kwamandan na dakarun Quds da kuma kwamandan mayakan Iraqi, Abu Mahdi al-Muhandis, sanadiyyar luguden wutar Amurka a Bagadaza.

Sai dai ofishin Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa zai koma gida da wuri daga Girka.

An umarci mambobin majalisar tsaron Netanyahu da kada suce komai dangane da kisan manyan mutanen, wanda jaridun Isra’ila suka bayyana da cewa kokarin kare ne daga ramuwar gayyar Iran da kawayenta a yankin.

Kawayen sun hada da ‘yan Hizbullah na Lebanon dake samun goyon bayan Iran, da kungiyar Hamas da ‘yan Jihadin Zirin Gaza.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − one =