Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa tace zata tabbatar da cewa masu shan wutar lantarki suna biyan kudin wutar da suka sha ta hanyar samar musu da mita.
Shugaban hukumar, Farfesa James Momoh, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja.
James Momoh yace hukumar za tayi dukkan abinda ya kamata wajen tabbatar da cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki sun samar da mitoci a karkashin shirin samar da mita.
An dauki matakin ne da nufin magance raguwar kudaden shiga da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke fama da shi.
Matakin zai kuma magance koke-koken jama’a akan yadda ake tsawwala musu kudin wuta karkashin tsarin yanke kudin wata ta hanyar hasashe.
Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta fitar da shirin samar da mita a watan Maris na 2018, a karkashin dokar gyaran bangaren wutar lantarki ta 2005.