Gwamnatin Zamfara Ta Ware Kudi Naira Biliyan 60 Domin Tituna A Shekarar 2020

76

Gwamnatin Jihar Zamfara tace ta ware kudi Naira Miliyan Dubu 60 domin gina tituna a fadin jihar a shekarar 2020.

Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Mayana, ya bayyana haka yayinda yake zantawa da manema labarai a Gusau, bayan kare kasafin kudin shekarar 2020 a majalisar dokokin jihar.

Ibrahim Mayana yace yawan dumbin kudaden da aka ware domin aikin tituna yayi nuni da cewa gwamnatin Bello Matawalle ta jajirce wajen samar da tituna ga jama’ar jihar, musamman mazauna yankunan karkara.

A cewarsa, za ayi amfani da kudaden wajen karasa ayyukan titunan da aka fara, tare da gina sabbin tituna a fadin jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa kasafin kudin shekarar 2020 na ma’aikatar zai kuma samar da kudade ga sauran ayyukan ma’aikatar, irinsu kula da tituna da harkokin sufuri.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − 8 =