
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya nanata kudirin gwamnatinsa wajen aiwatar da sabon karin Albashi ga Ma’aikatan jihar daga watan Fabreru na shakarar 2020.
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana haka ne a lokacin da yake rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Baba Malam Wali da kuma Sabbin Manyan Sakatarorin Ma’aikatu guda 8.
Haka kuma gwamnan ya bukaci wadanda aka nada dasu kasance masu ciyarda Ma’aikatunsu gaba, domin bunkasa jihar cikin gaggawa.
Haka kuma gwamnan, ya karbi Rahoton Kwamatin Ilimi na jihar, Inda ya bayyana cewa matsalolin yan kungiyar Boko Haram sun dakusar da cigaban Ilimi a jihar tsawon shekaru.
Kazalika ya ce Gwamnatin jihar ta fara aiwatar da Shawarwarin da kwamatin Ilimin ya bayar wadanda suka hada da bincike da kuma tantance yawan adadin Malaman Makarantar da suke jihar.