Gwamnatin Yobe Ta Kafa Kwamiti Domin Aiwatar Da Dokar Mafi Karancin Albashi

31

Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa kwamiti mai mutane 11 domin aiwatar da dokar mafi karancin albashi a jihar.

Shugaban ma’aikatan jihar mai rikon kwarya, Alhaji Muhammad Nura, ya bayyana haka cikin wata sanarwar da aka fitar a Damaturu.

A cewar sanarwar, kwamitin yana da Shugaban ma’aikata a matsayin Shugaba, yayinda sauran mambobin kwamitin suka hada da manyan sakatarori guda 6 da shugabannin kungiyoyin kwadago guda 4.

Manyan sakatarorin sune na ma’aikatun kudi, kasafin kudi da tsare-tsare, da na aikin gwamnatin da ayyukan yau da kullum, da na kananan hukumomin da masarautun gargajiya, inda babban sakataren ma’aikata ya zama magatakardar kwamitin.

Sauran mambobin sune Shugaban kungiyar kwadago ta jihar da Shugaban kungiyar kwadago yan kasuwa, da Shugaban kwamitin tattaunawa tsakanin gwamnati da yan kwadago da kuma sakataren kungiyar kwadago.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − 11 =