Gwamnatin Tarayya Zata Karfafa Masana’antun Cikin Gida Domin Su Samar Da Maganin Zazzabin Cizon Sauro

23

Jagoran shirin dakile zazzabin cizon sauro na kasa, Dr. Audu Mohammed, yace gwamnatin tarayya zata karfafa masana’antun cikin gida domin su samar da maganin zazzabin cizon sauro a kasarnan.

Ya gayawa manema labarai a Abuja cewa shirin zai aiwatar da hakan karkashin wani shirin hukumar lafiya ta duniya, WHO.

Yace shirin na hukumar lafiyar wanda aka kafa a shekarar 2011, wani shirine da hukumar lafiyar ta samar wajen inganta samun magunguna wadanda suka cika sharudan inganci domin maganin cuta mai karya garkuwar jiki, da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka.

Jagoran ya kara da cewa shirin ya nemi tallafin kudi daga masu bayar da tallafi guda uku, wadanda suka hada da bankin duniya da bankin cigaban musulunci da kuma bankin cigaban Afirka, domin tallafawa masana’antun wajen sayen magungunan zazzabin cizon sauron.

Dr. Mohammed daga nan sai yayi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su agazawa kokarin gwamnati na dakile zazzabin cizon sauro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × one =