Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan Naira Dubu 33 a matsayin alawus na wata-wata ga matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC).
Darakta Janar na hukumar matasa masu yiwa kasa hidima, NYSC, Birigediya Janar Shu’aibu Ibrahim, ya sanar da haka yayin zantawa da wasu matasa masu hidimtawa kasar a sakatariyar hukumar ta jihar Bauchi.
Janar Ibrahim wanda yake ziyarar aiki zuwa jihar, ya kawar da jita-jita dangane da yawan kudin da aka amince da shi a matsayin alawus na matasan.
Yayi bayanin cewa an samu amincewar ne bisa fara aiwatar da dokar mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta yi.
Janar Ibrahim yayi nuni da cewa, daga cikin yawan kudaden da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta, an amince da naira dubu 33 a matsayin sabon alawus din.