Gwamnatin Jihar Yobe Ta Bayar Da Tallafin Karatu Na Naira Miliyan 38 Da Dubu 400 Ga Wadanda Kuka Kammala Karatun Lauya

67

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu na kudi Naira Miliyan 38 da Dubu 400 ga wadanda suka kammala karatun lauya kuma za suje makarantun aikin lauya na Najeriya daban-daban dake kasarnan.

Gwamna Mai Mala Buni ya sanar da hakan a Damaturu yayinda ya mika cakin kudin ga hukumar tallafin karatu ta jihar.

Mala Buni yace wadanda za suci gajiyar su 69 zasu karbi kudaden da adadinsu yakai naira Miliyan 38 da Dubu 400.

A cewarsa, gwamnatinsa za kuma ta samawa wadanda suka ci gajiyar shirin da litattafai da komfutoci wadanda suke bukata wajen karatunsu domin samun nasara.

Mala Buni daga nan sai ya bukace su da su zamo jakadu nagari ga jihar.

Da yake mayar da jawabi, sakataren zartarwa na hukumar tallafin karatu ta jihar, Dr. Abubakar Kagu, ya yabawa kokarin gwamnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + twelve =