Daliban Da Ke Neman Rubuta Jarabawar JAMB sun Cika Makil A Helkwatar Hukumar Shaidar Zama Dan Kasa

69

Daliban da ke neman rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB sun cika makil a cibiyar number shaidar zama dan kasa dake helkwatar hukumar zama dan kasa a Abuja, domin samun number shaidar zama dan kasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa hukumar JAMB ta bukaci number shaidar zama dan kasa ga wadanda suke san rubuta jarabawar JAMB.

Sauran abubuwan da ta bukata sun hada da takardar haihuwa da takardar kammala Firamare da kuma number shaidar zama dan kasa ta iyaye ko marika, ga wadanda suke da shekaru kasa da 16 a duniya.

Daliban wadanda sukayi dafifi zuwa cibiyar, sun samu rakiyar malamansu, wadanda ke samun tallafin jami’an hukumar shaidar zama dan kasa, domin samun number kafin ranar karshe ta 17 ga watan Fabrairun gobe, wanda hukumar JAMB ta sanya domin rufe rijistar jarabawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 − two =