Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane 29 sanadiyyar zazzabin Lassa tare da wadanda suka kamu 195 a jihoshi 11 na tarayyar kasarnan.
Darakta Janar ta cibiyar, Dr. Chikwe Ihekweazu, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa wacce ya sanyawa hannu a Abuja, yayi bayanin cewa alkaluman na zuwa ranar Juma’a 24 ga watan Janairu ne.
Ihekweazu yace daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 89 cikin 100 sun fito ne daga jihoshin Onda da Edo da kuma Ebonyi.
Shugaban cibiyar yace karuwar kamuwa da cutar a wannan lokacin ba abin mamaki bane bisa la’akari da yanayin da ake ciki.
A cewarsa, ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya jagoranci wata tawagar kwararru zuwa jihar Kano a jiya Asabar, biyo bayan mutuwar wasu ma’aikatan lafiya 2 wadanda suka kamu da zazzabin na Lassa.