An Kashe Wata Bazawara Yar Shekara 20 a Jihar Jigawa

140

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa sun bankado gawar wata bazawara ‘yar shekara 20, mai suna Nafisa Hashimu, a kauyen Daneji, cikin yankin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa.

Kakakin rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Yace lamarin ya faru ne ranar 13 ga watan da muke ciki na Janairu, yayinda aka ga gawar matashiyar kwance a cikin daji a wajen kauyen na Daneji, mai nisan kilomita 22 daga garin Ringim.

Yayi bayanin cewa bayan samun labarin, ‘yansanda a ofishin ‘yanasanda na Ringim sun garzaya zuwa wajen tare da daukar gawar zuwa asibiti domin tantancewa, inda aka tabbatar da mutuwarta.

An mika gawar marigariyar zuwa ga iyalanta, kuma an binne kamar yadda addini musulunci ya tanadar. Abdu Jinjir yace an kaddamar da bincike sosai domin gano wadanda suka kashe ta tare da cafke su

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 4 =