Za Saka Yara Mata da Manyan Mata Dubu 20 a Makaranta a Sokoto

199

Akalla yara mata da basa zuwa makaranta da manyan mata dubu 20 ake sa ran shigarwa makarantun boko a kananan hukumomi 23 na jihar Sokoto.

Cynthia Obazee, jagora ta kasa ta wata kungiyar koyar da sana’o’i mai zaman kanta, mai suna GESA, ita shaida hakan a Sokoto.

Cynthia Obazee tayi jawabi a taron tuntuba na masu ruwa da tsaki akan sake bayar da damar ilimi ta biyu ga mata da yara mata.

Jagorar tace kungiyar ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya, UNESCO, ita ta basu kwangilar kaddamar da shirin a jihoshin Sokoto da Adamawa da Ebonyi da Cross River da Lagos, da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Cynthia Obazee tace kungiyar ta GEZA tare da hadin gwiwar hukumar ilimin manya, karkashin ma’aikatar ilimi, da sauran hukumomin dake da alaka, zasu kaddamar da bayar da damar ilimi ta biyu ga mata da yara mata a kananan hukumomin Sokoto ta Arewa da Binji.

A cewarsa, za a fadada shirin zuwa sauran kananan hukumomin a shekarar 2020.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 5 =