Za A Rubuta Jarabawar JAMB Tsakanin Ranakun 14 Ga Watan Maris Zuwa 4 Ga Watan Afrilu na 2020

84

Hukumar jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa, JAMB, tace zata gudanar da jarabawar shiga manyan makarantu ta shekarar 2020 tsakanin ranakun 14 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Afrilu.

Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka yayinda yake ganawa da kwamishinonin ilimi na jihoshin kasarnan a Abuja.

Oloyede yace za a fara rijistar jarabawar gwaji tsakanin ranakun 13 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa, yayinda za gudanar da jarabawar ta gwaji a ranar 18 ga watan Fabrairu.

Yayi bayanin cewa za gudanar rijistar jarabawar ta shiga manyan makarantu da kuma ta wadanda suka kammala makarantar gaba da sakandire suna neman shiga jami’a wato D.E a lokaci guda, tsakanin ranakun 13 ga watan Janairu zuwa 17 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

A cewarsa, hukumar ta shigo da hukumar shaidar zama dan kasa a harkar jarabawar shiga manyan makarantu ta shekarar 2020, kamar yadda majalisar kasa da majalisar zartarwa ta tarayya suka bayar da umarni.

Daga nan sai ya umarci masu san rubuta jarabawar da su je cibiyoyin rijista na hukumar shaidar zama dan kasa domin samun numbar shaidar zama dan kasa saboda su samu damar yin rijistar jarabawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − five =