‘Yansanda Sun Kama Wani Sanannen Mai Satar Mutane Dan Shekara 20 a Katsina

79

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina sun kama wani sanannen dan tawagar masu satar mutane, dan shekara 20, Aliyu Sani, mazaunin sabuwar unguwa a birnin Katsina.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, shine ya bayyana haka yayin taron manema labarai wanda aka gudanar a yau a Katsina.

Yace matashin tare da yan tawagarsa sun sace mutane tare da kai su dajin Gora, cikin yankin karamar hukumar Batsari, domin neman kudin fansa.

Gambo Isah yace ‘yansanda sun kama mutane 3 saboda aikawa da sakon barazana tare da kiran wayar wani mai suna Shu’aibu Bala, dan shekaru 36, mazaunin Gozaki a karamar hukumar Kafur, inda suke razana shi.

A cewarsa, dakarun operation puff adder, karkashin jagorancin DPO na Kafur, sun samu nasarar kama ‘yan tawagar a kauyen Unguwar Iliya dake Kafur, yayinda suka je karbar kudin fansa na Naira Dubu 150.

Yace da aka tsananta bincike, an kwato shanu 23 daga hannunsu, wadanda ake zaton satowa suka yi. Kakakin na ‘yansanda yace wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − three =