‘Yan Shi’a Sun Halarci Bautar Kirsimeti A Wata Coci A Jihar Kaduna

215

Wata tawagar ‘yan kungiyar yan’uwa musulmai ta Najeriya, wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, sun halarci bauta a wata coci dake Samaru a Zariyan jihar Kaduna.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bautar, jagoran tawagar, Farfesa Isa Hassan Mshelgaru, yace manufar halartar bautar shine dabbaka kauna, hakuri da fahimtar juna tsakankanin yan Najeriya.

Hassan-Mshelgaru sai ya roki ‘yan Najeriya, musulmai ko kirista ko mabiya addinan gargajiya, da su kauracewa dukkan nau’in kiyayya, inda yace addini ba a gina shi akan doron kiyayya ba, sai dai hanyar hada kawunan mutane waje guda.

Limamin cocin, Reverend Isuwa Sa’idu, ya bayyana godiya bisa halartar tasu, inda ya bukace da su cigaba da hakan domin amfanin kasarnan.

Yace bikin ya wayarwa da mutane kai wajen fahimtar cewa yan Najeriya suna da damar zama cikin lumana tare da juna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 10 =