Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Baki ‘Yan Kasashen Ketare 2 da Wani ‘Dan Najeriya a Jihar Neja

202

‘Yansanda a jihar Neja sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace wasu yan kasashen ketare 2 da wani dan Najeriya ma’aikacin kamfanin gine-gine na Triacta a kauyen Galadima Kogo, a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Mallam Adamu Usman, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a yau a Minnna, yace ‘yan bindigar wadanda ke sanye da kayan sarki sun zo kauyen akan babura sama da 20 inda suka farwa ma’aikatan kamfanin.

Adamu Usman yace lamarin ya auku ne a yau Talata da misalin karfe 1 na rana.

Yace rundunar ‘yansanda sun kaddamar da sumame domin kamo wadanda suka kai farmakin tare da ceto wadanda aka sace.

Daga nan sai ya roki mutanen kauyen da su kai rahoton duk wata bakuwar fuska ga hukumomin tsaro mafi kusa da su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 7 =