Rundunar Tabbatar Da Yaki Da Rashin Da’a A Jihar Borno Ta Horas Da Masu Aikin Sa Kai 2,700

53

Rundunar tabbatar da yaki da rashin da’a a Jihar Borno ta ce ta horas da masu aikin sa kai su 2,700, domin su bada gudummawar cigaban al’umma a fadin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa bada horan an samar da shi ne da hadin gwiwar hukumar wayar da kan al’umma ta kasa da kuma ma’aikatar sufuri, matasa da samar da aikin yi da kuma Gwamnatin jihar Borno.

Daraktan hukumar ta jihar Alhaji Yahaya Imam, ya bayyana hakan a lokacin bikin yaye wadanda aka ba wa horon a Maiduguri.

Ya ce masu aikin sa kan an horadda da su a banagaren tsaro da kuma dabarun yadda za su gudanar da ayyukansu.

Imam ya bayyana horan da cewa shi ne na farko da aka gudanar a shekaru goma da suka gabata, inda ya ce masu aikin sa kan an kuma horadda da su akan dabaru ta yadda za su shawo kan masu aikata laifuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − five =