Shirin samar da abinci na duniya yace zai fadada ayyukan bayar da agajinsa a kasar Zimbabwe, saboda rabin ‘yan kasar na fama da tsananin yunwa, sanadiyyar sauyin yanayi da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
A cewar shirin, zafi na karuwa zuwa fiye da ninkin yadda ya kamata, kuma an samu fari da ambaliyar ruwa a yankunan birane da karkara.
Sanarwar hakan ta fito ne kwanaki kadan bayan dan jaridar majalisar dinkin duniya akan samar da abinci, Hilal Elver, yayi kira ga kasashen yamma su dage takunkuman da suke kakabawa kasar ta Zimbabwe, inda yace suna taimakawa wajen tura kasar zuwa fadawa masifar yunwa.
Kasashen yamma sun kakabawa kasar ta Zimbabwe takunkumai akan take hakkin bil’adama, zamanin mulkin tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe.