Ma’aikatar Lafiya ta Tarraya tace tana daukar matakan inganta magungunan gargajiya a kasarnan.
Hajiya Zainab Shariff, daraktar sashen magungunan gargajiya a ma’aikatar lafiya ta tarayya, ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Abuja.
Yace majalisar lafiya ta kasa ta amince da kafa sashen magungunan gargajiya a ma’aikatun lafiya na jihoshi 36 da babban birnin tarayya.
Daraktar ta kara da cewa, matakin zai habaka aikin magungunan gargajiya a kasarnan.
Ta bayyana cewa masu samar da maganin gargajiya 32, majalisar magunguna da lafiyar hakora ta Najeriya ta yiwa rijista tare da basu lasisi, kamar yadda doka ta sahale.