Jihar Borno ta Ware Kudi Naira Biliyan 23 Ga Bangaren Ilimi a Kasafin Kudin Badi

43

Gwamnatin jihar Borno ta ware kudi Naira Biliyan 23 ga bangaren ilimi a kasafin kudin badi, domin farfado da bangaren tare da magance akidar Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, an warewa bangaren adadin kudin a kasafin kudin jihar na badi na naira biliyan 135 da miliyan 500 wanda gwamnan jihar, Babagana Zulum, ya gabatarwa majalisar.

Wasu daga cikin bayanan tanadin kasafin kudin, sun hada da kashe kudi Naira Biliyan 6 da Miliyan 941 domin sayar da gine-gine da bencina, da horas da malamai tare da samar da kayayyakin koyo da koyarwa a karkashin ma’aikatar ilimi.

Sauran ayyukan da za ayi sun hada da gina manyan makarantun 2 da makarantun fasaha 2 a Wuyo, da Chibok, da Mbalala da kuma Bulabulin.

Sannan za a gyara makarantun sakandire dayawa a Monguno; da Damasak, da Gajiram, da Gubio, da Dikwa, da Ngala, da Konduga, da Bama da kuma Gwoza.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − eleven =