Jami’an Kwastan Sun Kai Sumame a Adamawa Domin Shinkafa Yar Waje

144

Jami’an hukumar hana fasa kwauri a garin Mubi tare da jami’an hukumar na Adamawa da Taraba, sun kai sumame zuwa kasuwar garin Mubi domin kame shinkafar kasashen ketare, da sauran kayayyaki jabu a jihar Adamawa.

Kamfanin Dillancin Labarai ya bayar da rahoton cewa, sumamen karkashin Comptroller, Kamardeen Olumoh, ya jawo kame buhunhuna dayawa na shinkafa yar waje tare da kame mutane uku da ake zargi.

Jami’an hukumar, tare da hadin gwiwar yansanda, sun kai farmaki zuwa babbar kasuwar garin dake kan iyaka da misalin karfe 11 na safe, inda suka yashe shaguna da dama.

Da yake jawabi akan cigaban da aka samu, comptroller na hukumar a shiyyar, yace sumamen ya biyo bayan umarnin shugaban hukumar dake Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × two =