Hukumar Tara Haraji Ta Jihar Kaduna Ta Tara Sama Da Naira Biliyan 44 a Shekarar 2019

42

Hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kaduna tace jihar ta tara kudi sama da naira miliyan dubu 44 a matsayin kudaden shiga a shekarar da muke ciki ta 2019.

Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoton ayyukan hukumar na shekara a wajen taron manema labarai a Kaduna.

Zaid Abubakar yace kudaden da aka tara sun haura yawan kudaden da aka sa ran tarawa na naira miliyan dubu 43, da karin naira miliyan dubu 1.

Zaid Abubakar yayi nuni da cewa wannan shine karon farko da jihar ta cimma tara yawan kudaden da ake sa ran tarawa, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara, kuma wani sabon matsayi wajen tara kudaden shiga a jihar.

Daga nan sai ya danganta nasarar da aka samu ga gudunmawa da goyon bayan gwamna Nasir El-Rufa’i, wajen bayar da dama ga hukumar tayi aikin ba tare da takura ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − nine =