
Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe kudi sama da Naira Miliyan 208 wajen biyan kudaden jarabawar WAEC ga dalibai 21,589 a wannan shekarar da muke ciki.
Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Badamasi Lawal, shine ya bayyana haka a Katsina, yayin da yake zantawa da manema labarai.
Yace dalibai 7,276 daga cikin 21,589, kashi 50 cikin 100, na wadanda suka zauna jarabbawar sun samu credits 5 zuwa sama, wadanda suka hada da Lissafi da Turanci.
A cewarsa, dalibai 14,481, kashi 66 cikin 100, sun samu credits 5 zuwa sama a wasu darussan daban.
Badamasi Lawal ya danganta nasarar da jajircewar gwamnati wajen bunkasa cigaban gine-gine a makarantu, da daukar malaman makaranta, da bayar da horo, tare da samar da kayan aiki, da sauransu.
Kwamishinan daga nan sai ya bayyana cewa ana samun cigaba a jarabawar dalibai tun bayan kafuwar gwamnati mai ci a shekarar 2015.