Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da kashe kudi sama da naira biliyan 2 da miliyan 500 domin ginawa tare da daga martabar asibitoci 4 a sabbin masarautu 4 da aka kirkiro.
Sabbin masarautun da aka kirkiro sune na Karaye da Rano da Bichi da kuma Gaya.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Mallam Muhammad Garba ya rabawa manema labarai a Kano, yace amincewar na daga cikin abubuwan da aka zartar yayin zaman majalisar wanda aka gudanar a majalisar dake gidan gwamnati a Kano.
Kwamishinan ya kuma kara bayyana cewa majalisar ta kuma amince da bayar da kwangilar samar da kayan aiki a cibiyar kula da cutar daji, kansa, da ake ginawa, akan kudi sama da naira biliyan 4 da miliyan 200, domin inganta kiwon lafiya a jihar.
Kwamishinan yace majalisar ta kuma amince da samar da makarantar yanmata ta kimiyya da fasaha ta kwana a garin Ganduje cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, akan kudi naira miliyan 162 da dubu 200, tare da amincewa da fitar da kudi naira miliyan 30 da dubu 600 domin daukar bakuncin taron majalisar matasan Najeriya na farko.